<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>63</hymn_number>
<title>Can Wani Tudu Bayan Gari, Ka Yanka Sadaka LW63</title>
<lyrics>[V1]
 1) Can wani tudu bayan gari, ka yanka sadaka,
 Ka ba da rai mai tsarki mai kawo gafara.

[V2]
 2) Ran Yesu ne Allah ya sa ya fanshi namu rai.
 Mai isa shafe laifinmu da jininsa kaɗai.

[V3]
 3) Mun kasa biyan bashinmu, nan duniya ba mai biya.
 Mai buɗe ƙofar rai, sai shi, Mai Ceto, Mai Shari'a.

[V4]
 4) Ba za mu iya kwatanta iyakar ƙauna ba.
 Alhakinmu mai girma dai, ya karye zuciyarsa.

[V5]
 5) Ai, za mu naɗa Sarkin nan, mu shiga bautarsa.
 Har zuwa iyakar duniya mu kafa mulkinsa</lyrics>
</song>